A cewar rahoton da firayiministan kasar Li Keqiang ya sahale tare da rattabawa hannu, kasar za ta fuskanci wani gagarumin sauyi tsakanin shekarar 2021 da 2030, inda za a samu raguwar adadin mutane dake cikin shekarunsu na aiki, da yawaitar wadanda shekarunsu ya ja, da kuma masu kaura.
Rahoton ya ce kasar za ta rungumi tsarinta na kayyade iyali, inda za ta aiwatar da tsarin haihuwar 'ya'ya biyu ga kowane iyali domin cike gibin dake akwai.
Ya kara da cewa, gwamnati za ta inganta tsarin haihuwa, sannan za ta kyautata yanayin aikin gwammnati tare da tallafawa iyalai ta yadda za a cimma muradin da aka sanya gaba.
Har ila yau, za a dauki matakan da suka hada da karfafa kaura zuwa birane, inganta tsarin zirga-zirgar al'umma, magance matsalar yawan mutane da shekarunsu suka ja, inganta walwalar mata da kuma kare yara da masu bukata ta musammam. ( Fa'iza Mustapha)