Alkaluman da ma'aikayar ta fitar sun nuna cewa a shekarar ta 2017, adadin jari na kai tsaye da kasar ta samu ya karu da kaso 7.9 bisa dari, hakan kuwa ya biyo bayan manufofin kasar na kara bude kofa ga kasashen waje, da kyautata damammakin zuba jari a kasar.
Karin da aka samu na 7.9 bisa dari a bara, ya kai kimanin kudin Sin biliyan 877.56, wato kimanin dalar Amurka biliyan 136.33.
Sanarwar ta kara da cewa, a bara yawan sabbin kamfanonin kasashen waje da aka yiwa rajista a kasar sun kai 35,652, adadin da ya karu da kaso 27.8 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar da ta gabaci hakan.
Wani jami'in ma'aikatar ya alakanta nasarar da aka samu da kyakkyawan yanayin zuba jari, da manufofi dake bada cikakkiyar damar shigowar jarin waje daga masu zuba jari na kasashen ketare.
Ya ce a baran, gwamnatin Sin ta yi namijin kokari wajen saukaka hanyoyin zuba jarin waje, wanda hakan ya samar da nasarori da dama musamman a fannin bada hidima ta fuskar fasahohin zamani, adadin da ya kai kaso 93.2 bisa dari sama da na shekarar da ta gabaci hakan, yayin da kudin da aka zuba ya kai kudin Sin Yuan biliyan 184.65.(Saminu Alhassan)