in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan tattaunawa tsakanin Koriya ta kudu da ta arewa
2018-01-18 20:09:34 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kasar sa na goyon bayan aniyar koriya ta kudu da koriya ta arewa, game da hawa teburin shawarwari, a wani mataki na gina yarda da juna, da cimma daidaito, ta yadda za a kai ga warware matsalar da sassan biyu ke fuskanta ta hanyar lumana.

Mr. Lu Kang ya ce cimma wannan daidaito tsakanin kasashen biyu zai kyautata alakar su, tare da sassauta yanayin da ake ciki a zirin koriya. Daga nan sai ya sake kira ga sassan biyu da su martaba wannan dama, kana suma sassan kasa da kasa su yi amfani da zarafin wajen goyon bayan wanzar da zaman lafiya, da kuma daukar matakan kawo karshen cece ku ce.

A ranar Larabar makon jiya ne dai koriyar biyu suka cimma matsaya game da kyale tawagar koriya ta arewa halartar wasannin gasar Olympic da za a gudanar a birnin Pyeongchang dake koriya ta kudu.

A wani ci gaban kuma, ministan harkokin wajen koriya ta kudu Kang Kyung-wha, ya ce kasar sa za ta ci gaba da ingiza batun tattaunawa, ta yadda za a kai ga warware matsalar makaman nukiliya a zirin koriya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China