in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan Sinawa masu shekaru 100 a Beijing ya karu
2017-10-30 20:09:31 cri
Wani rahoton hadin gwiwa da gwamnatin birnin Beijing da wata cibiyar bincike ta kasar Sin suka fitar a yau Litinin ya nuna cewa, yawan Sinawa masu shekaru 100 a duniya dake zaune a kwaryar birnin Beijing ya karu zuwa 751 a shekarar 2016, adadin da ya dara na shekarar da ta gabata da mutum 43.

Rahotron ya ce a shekarar 2016, matsakaicin tsawon rayuwar mazauna birnin na Beijing shi ne shekaru 82 da watanni uku, sama da kaso 0.68 a shekara daga shekarar 2012.

Yanzu haka, yawan tsofaffi a kasar Sin na karuwa sosai, kuma ana fatan yawansu zai kai miliyan 400 nan da karshen shekarar 2035, kamar yadda hukumar kula da tsaron jama'a ta kasar Sin ta bayyana. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China