Jami'in MDD a kasar Kenya Siddharth Chatterjee, ya fadawa taron dandalin shiyya da aka gudanar a Nairobi dangane da batun ci gaban al'umma cewa, cigaban tattalin arzikin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata sakamako ne na yadda ya zuba jari kan harkokin matasa.
Chatterjee, ya fada a lokacin bude taron dandalin cigaban al'umma na Sin da Afrika karo na farko cewa, Afrika zata iya amfani da matasanta wajen ba su horo a fannoni daban daban domin bunkasa cigaban tattali arzikin kasa.
Taron na wuni biyu, zai taimaka wajen karfafa mu'amala tsakanin Afrika da Sin ta fuskar cigaban al'umma.
Chatterjee yace, Afrika tana bukatar samar da guraben aiki miliyan 100 a kowace shekara har na tsawon shekaru 10 masu zuwa, hakan zai samar da gagarumin cigaba idan aka yi amfani da yawan al'ummar da nahiyar kedashi.
Kana ya ce kasar Sin ta zama abin misali cikin kasashen duniya masu tasowa ta fustar tsara yanayin iyali.