A wajen taron manema labaru da aka kira yau a birnin Beijing na kasar Sin, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, "a ranar Talata, kasashen Canada da Amurka sun yi kira ga wasu kasashen da su ma suka taba tura sojoji don halartar yakin da aka yi a zirin Koriya a shekarar 1950, su gudanar da wani taron ministocin harkokin waje a birnin Vancouver na kasar Canada, inda ake da niyyar matsawa kasar Koriya ta Arewa lamba iya bakin kokarinsu, to, mene ne ra'ayin kasar Sin dangane da batun?"
Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya amsa da cewa shawarar da Canada da Amurka suka gabatar ta nuna ra'ayinsu na tsohon yayi irin na yakin cacar baki, wanda zai janyo baraka tsakanin gamayyar kasa da kasa kawai, maimakon taimakawa daidaita batun nukiliyar zirin Koriya.(Bello Wang)