A cewar Wang Pei'an, mataimakin shugaban hukumar lafiya da tsarin iyali ta kasar, ana ganin bayan an daidaita wannan tsari, yawan haihuwa zai karu zuwa wani matsayi a shekaru masu zuwa kuma za'a samu karin haihuwa kusan miliyan 20 a shekarar koli dake tafe.
Jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar bayan wani taron da ta yi a ranar Alhamis din da ya gabata ta sanar da cewa kasar za ta amince ma'aurata su haifi yara biyu, abin da ya nuna cewa ta jinginar da tsarin haihuwa daya da take bi na shekaru masu yawa a baya.
Kusan ma'aurata miliyan 90 yanzu za su cancanci kara haihuwa na biyu idan aka kamala yin gyara a tsarin, in ji Mr Wang, yana mai cewa, an yi kiyasin kusan a cikin mata wadanda suka cancanci hakan kashi 60 a cikin 100 suna kasa da shekaru 35 ku fi.
A bisa kiyasin hukumar kididdigar ta kasar, Sin tana da yawan al'umma biliyan daya da miliyan 368 (1.368 billion) a karshen shekara ta 2014. (Fatimah Jibril)