in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun karuwar tsofaffi a kasar Sin
2016-07-11 20:07:47 cri
Ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayyana a cikin rahoto cewa, a karshen shekarar 2015 akwai mutane miliyan 222 masu shekaru 60 zuwa sama a kasar, wato kwatankwacin kashi 16.1 cikin 100 na yawan al'ummar kasar.

Wannan adadi ya nuna karuwar kashi 0.6 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata, lokacin da mahukuntan kasar suka ba da rahoton cewa, akwai mutane miliyan 212.4 masu shekaru 60 zuwa sama a cikin kasar.

Rahoton da ma'aikatar ta fitar na nuna cewa, cikin mutane miliyan 222, miliyan 143.86 daga cikinsu shekarunsu 65 ne ko kuma fiye da haka ko kuma kashi 10.5 cikin 100 na yawan al'ummar kasar. Bugu da kari, sama da kashi 10.1 cikin 100 na adadin shekarar 2014. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China