in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana fatan yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka da sauran kasashen duniya wajen yaki da sayen dabbobi da itace ba bisa doka ba
2018-01-18 20:17:56 cri
Tun daga ranar 1 ga watan Janairu na bana, an haramta dukkanin wani nau'i na cinikayyar hauren giwaye. Kasashen Afirka sun nuna yabo ga wannan kuduri.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Alhamis cewa, a matsayin kasar da ta sa hannu kan yarjejeniyar da ta jibanci cinikayyar dabbobi da itace ta duniya, kasar Sin na sauke nauyin dake kanta na yarjejeniyar. Kaza lika kasar ta Sin na fatan ci gaba da kokari tare da kasashen Afirka, da sauran kasashen duniya wajen yaki da sayen dabbobi, da itace ba bisa ka'ida ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China