in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin duniya zai bunkasa sosai a bana
2018-01-18 09:47:58 cri
A jiya Laraba ne, a birnin Landan na kasar Birtaniya, dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya ya bullo da wani rahoto kan hadarrukan da duniya ka iya fuskanta a shekara ta 2018, inda aka yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai bunkasa sosai a bana, al'amarin da zai samar da kyakkyawar dama ga shugabannin kasashe daban-daban, ta yadda za su warware matsaloli da kalubaloli da al'ummominsu ke fiuskanta a tattalin arziki, dangantakar kasa da kasa, muhalli da makamantansu.

A kan wallafa rahoto kan hadarrukan da duniya ka iya fuskanta a watan farko na kowace shekara, inda kwararru da mahukunta daga fadin duniya ke bayyana ra'ayoyinsu dangane da manyan hadarrukan da duniya ka iya fuskanta. Kimanin mutane dubu daya ne suka halarci taron jin ra'ayin jama'a da aka kira kan hadarrukan da duniya ka iya fuskanta a bana, ciki har da kashi 59 bisa dari na mutane da ke ganin cewa, hadarurrukan za su karu, kana, akwai kashi 7 bisa dari kawai wadanda ke cewa, hadarrukan za su ragu.

Jagoran dandalin tattaunawa na tattalin arzikin duniya, kana, shugaban zartaswa na dandalin na yanzu, Dr. Klaus Schwab ya bayyana cewa, farfadowar tattalin arzikin duniya na samar da zarafi mai kyau ga duniya baki daya, wajen lalubo bakin zaren daidaita kalubalolin da suka shafi tsare-tsare, zaman rayuwar al'umma da muhalli. Haka kuma, ya kamata kasashe daban-daban su zama tsintsiya madaurinki daya, domin tinkarar duk wani hadarin da ka iya kunno kai a fadin duniya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China