Yadda kasar Sin ta bunkasa tattalin arzikinta zai ba da taimako wajen samun ci gaba mai dorewa
Masanin tattalin arziki na bankin duniya Franziska Lieselotte Ohnsorge, ya bayyana a ranar 9 ga wata cewa, yadda kasar Sin ta bunkasa tattalin arzikinta yanzu zai ba da taimako wajen samun ci gaba mai dorewa.
Bankin duniya ya gabatar da rahoton hasashen tattalin arizkin duniya na ranar 9 ga wata, inda aka bayyana cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin zai ragu daga kashi 6.8 cikin dari a shekarar 2017 zuwa kashi 6.4 cikin dari. (Zainab)