in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin za su gina layin dogo a Nijeriya
2017-08-18 11:08:09 cri
Ministan sufuri na Nijeriya Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa ta fara aiwatar da aikin gina layin dogo, aikin da ake fatan zai lashe dallar Amurka biliyan 41.

Bisa shirin da aka tsara, za a gina wani sabon layin dogo mai tsawon kilomita dubu daya da dari daya a tsakanin birnin Lagos da birnin Kano, da kuma wani layin dogo a wanda zai tashi daga birnin Lagos zuwa birnin Calabar. Kuma bisa hasashen da aka yi, gaba daya za a kashe dallar Amurka biliyan 20 kan wadannan layin dogo guda biyu, Kuma an samu galibin kudaden gudanar da wadannan ayyuka ne daga bankin shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin, watau EIBC.

Bugu da kari, Mr. Amaechi ya bayyana cewa, kamfanin CCECC na kasar Sin zai gudanar da ayyukan gina layukan dogon biyu, wanda ake fatan kammala shi a karshen shekarar 2019. Kamfanin kayayyakin wutar lantarki na GE kuma, zai jagoranci kamfanoni guda uku da suka hada da kamfanin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa na kasar Sin, kamfanin sufuri na kasar Afirka ta Kudu da kuma kamfanin APM na kasar Holland, wajen gudanar da aikin gyara layin dogo maras fadi mai tsawon kilomita 3505 tsakanin birnin Lagos da tashar jirgin ruwa ta Fatakwal. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China