in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin Sin ya kaddamar da nazari kan wani jirgin kasa da zai iya saurin gudun kilomita 600 a duk awa guda
2016-10-23 12:07:14 cri

Wani kamfanin kasar Sin zai kaddamar da bincike da bunkasawa kan wani jirgin kasa dake aiki da maganadisu (maglev) da zai iya gudun kilomita 600 duk awa guda, wanda zai kasancewa mafi saurin gudu fiye da sauran jiragen kasa dake da gudu kan maganadisu da a halin yanzu suke aiki.

Kamfanin CRRC, babban kamfanin kera kayayyakin sufurin jiragen kasa na Sin, ya sanar cewa zai yi shirin kera wani layin jirgin kasan maglev na a kalla tsawon kilomita biyar a matsayin gwaji na sabon jirgin kasan.

Kamfanin zai bunkasa kuma jiragen kasan maglev da zasu iya gudun kilomita 200 a duk awa guda, tare da burin kafa tsare tsaren fasaha da ka'idojin kasa domin wani sabon zamanin sufurin maglev na matsakaici da gudun gaske, da zai iya aiwatar dasu a dukkan fadin duniya, in ji Sun Bangcheng, wani jami'in CRRC.

Haka kuma, kamfanin zai kaddamar da bincike da bunkasawa kan jiragen kasa masu saurin gudu na kan iyakoki, da zasu iya gudun kilomita 400 a duk awa gudu da sauyawa tsakanin nau'o'in hanyar layin dogo da ta tashi daga santimita 60 zuwa mita 1,676.

Irin wadannan jiragen kasa zasu shan wutar lantarki kashi 10 cikin 100 kasa da wanda jiragen kasa masu saurin gudu na kilomita 350 a duk awa gudu suke sha da suke aiki a halin yanzu, in ji mista Sun. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China