Ministan wanda ya bayyana hakan bayan da aka zagaya da shi cikin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, ya bayyana tabbacin cewa,kamfanin yana da kwarewar gudanar da wannan aiki.
Bugu da kari, minista Ameachi ya ce za a kammala aikin layin dogo daga Lagos zuwa Kano nan da shekaru biyu masu zuwa. Aikin da a cewarsa zai taimaka wajen samar da guraben aikin yi 250,000 ga 'yan Najeriya.
Ministan ya kuma shaidawa manema labarai cewa, kamfanin na kasar Sin zai bude cibiyar horas da 'yan Najeriya game da fasahohin da suka shafi gudanar da ayyuka, kula da na'urori da kuma harkokin sadarwa.
Ya ce, gewamnatin Najeriya za ta tabbatar da cewa, farashin tikitin jirgin kasan bai gagari talaka ba.(Ibrahim)