Bikin ya samu halartar jakadan kasar Sin a tarayyar Nijeriya, Mr.Zhou Pingjian da dukkanin ma'aikatan ofishin jakadancin da jami'ai daga sassan gwamnati da hukumomin tsaro na Nijeriya da ma wakilan tawagar jakadun kasashe daban-daban da na hukumomin kasar Sin da Sinawa mazauna kasar sama da 400.
A jawabin da ya gabatar, Mr.Wang Runxu ya bayyana tarihin bunkasuwar rundunar sojan kasar Sin, musamman ma nasarorin da aka cimma a wajen gyare-gyare tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18.
Har wa yau, Jami'in ya kuma bayyana aikin da rundunar sojan kasar ta gudanar wajen aiwatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD da kuma ba da kariya ga jiragen ruwa da ke zirga-zirga a mashigin tekun Aden. Baya ga haka, Wang Runxu ya kuma waiwayi nasarorin da kasashen Sin da Nijeriya suka cimma ta bangaren hadin gwiwar ayyukan soja cikin shekarun baya, tare da bayyana niyyar inganta hadin gwiwar.
Daga nasa bangaren, wakilin ma'aikatar tsaron tarayyar Nijeriya, Manjo John Enenche, ya yaba wa kasar Sin bisa irin ci gaban da rundunar sojin ta samu, inda kuma ya mika godiya ga gwamnati da rundunar sojin ta kasar Sin bisa tallafi da goyon bayan da suke bayarwa. (Lubabatu)