An kafa cibiyar nazarin al'amuran Afirka ta jami'ar horar da malamai ta lardin Zhejiang(ISAZNU) ne a watan Satumban shekarar 2007 karkashin kulawar ma'aikatun Ilimi da na harkokin wajen kasar Sin.
Cibiyar na da masu bincike na din-din-din sama da ashirin wadanda ke gudanar da bincike a fannoni daban-daban kamar harkokin siyasar Afirka,da hadin gwiwar kasa da kasa, tattalin arziki, tarihi, da al'adun Afirka.
Darektan cibiyar Liu Hongwu ya ce, cibiyar tana kuma hadin gwiwa da jami'o'i da masana, cibiyoyin bincike da kafofin watsa labarai na nahiyar Afirka da nufin cimma nasarar manufofin da aka sanya a gaba.(Ibrahim Yaya)