Mahukuntan kasar Sin sun bayyana shirin fara gina karin layukan dogo 35 a wannan shekara ta 2017. Hakan dai wani bangare ne na fadada sufurin jiragen kasa a wasu karin sassan kasar daban daban. Ana sa ran fara ginin layukan dogo da tsayin su zai kai kilomita 2,100, da tagwayen layuka 2,500, da kuma masu amfani da wutar lantarki 4,000.
Tuni dai aka warewa kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar CRC zunzurutun kudi har Yuan biliyan 800, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 116.8 a matsayin kasafin kudin ayyukan kamfanin na bana.
Da yake karin haske game da ci gaban da ake hasashen samu a wannan fanni, mataimakin ministan ma'aikatar sufurin kasar Sin Yang Yudong ya ce, karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, wato tsakanin shekara 2016 zuwa 2020, Sin za ta kashe kudi har Yuan Tiriliyan 3.5 a fannin ginin layukan dogo. Kaza lika nan da shekarar 2020, za a kai ga tsawaita layukan dogon dake kasar zuwa kilomita 30,000, layukan da tsayin su zai kai ga ratsa kaso 80 bisa 100 na daukacin manyan biranen kasar.
Ya zuwa karshen shekarar bara, tsayin layukan dogo na kasar Sin ya kai kilomita 124,000, ciki hadda masu daukar jiragen kasa mafiya sauri, wadanda tsayin su ya kai kilomita 22,000. Layukan da kuma suke sahun gaba ta fuskar tsayi a dukkanin fadin duniya.(Saminu)