Mai rikon mukamin mataimakin shugaban majalisar 'yan kasuwa da masana'antu ta kasar Kenya James Mureu ya bayyana cewa, sabon layin dogo da kamfanin kasar Sin ya gina a kasar Kenya (SGR) na iya taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Mureu ya shaidawa taron manema labarai gabanin makon bikin baje kolin kayayyaki na kasar Sin dake tafe cewa, sabon layin dogon mai tsawon kilomita 480 wanda ya tashi daga Nairobi zuwa birnin Mombasa mai tashar jigaren ruwa zai saukaka zirga-zirgar kayayyakin da ta jama'a tsakanin manyan biranen biyu.
Ya kuma bayyana cewa, suna fatan sabon layin dogon zai kara bunkasa harkokin tattalin azriki, ta hanyar inganta al'amura a kasar.(Ibrahim)