Bikin ya samu halartar Mataimakin darektan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasa Sin Guo Weimin da shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar dattawan Nijeriya Suleiman Adokwe da wasu Ministocin kasar.
Za a gudanar da gwajin a Nijeriya ne ta hanyar amfani da fasahohi da na'urorin kasar Sin, domin ba al'ummomin kasar damar kallon talebijin dake aiki da tauraron dan Adam, tare da kara musu hanyoyin samun labarai.
A sa'i daya kuma, ana sa ran shirin zai iya karfafa zumunci da fahimtar juna a tsakanin al'ummomin kasar Sin da na Nijeriya. (Maryam)