Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana a ranar Litinin da sahihin goyon bayansa ga layin dogo na zamani samfurin SGR da aka gina tsakanin birnin Mombasa na kasar Kenya dake bakin teku da babban birnin kasar, Nairobi, wanda kasar Sin ta zuba kudin ginawa.
Da yake ziyarar aiki a yankin aikin na SGR dake karkarar Nairobi, tare da rakiyar ministoci da dama, mista Sall ya bayyana cewa, wannan babban aiki zai taimaka ga tsarin kawo sauyin tattalin arziki da na al'umma a nahiyar Afrika.
Kasar Sin na kawo wata muhimmiyar gudummuwa ga bunkasuwar tattalin arzkin Afrika ta hanyar ci gaban ababen more rayuwa. Muna bukatar hanyoyi, layukan dogo, gadoji da kuma tashoshin samar da wutar lantarki domin cimma bunkasuwa a nahiyar Afrika, in ji mista Sall.
Manyan jami'an Kenya da jakadan kasar Sin dake Kenya, Liu Xianfa, sun marawa shugaban kasar Senegal a yayin rangadin nasa domin kimanta ci gaban da aka samu wajen aiwatar da aikin na SGR.
Haka kuma an samu halartar kwararrun kamfanin gina hanya da gada na kasar Sin CRBC dake gudanar da wannan aikin gina layin dogo mai saurin gudu na tsawon kilomita 472.
Layin dogon na zamani da kasar Sin ta zuba kudin ginawa shi zai hada kasar Kenya da kasashe makwabta, kuma wannan zai ba da misali ga sauran kasashen Afrika dake bukatar gina irin wannan layin dogo na zamani a nan gaba, in ji Macky Sall.
Ya kara da cewa, "Ina farin ciki da ci gaban da aka samu ga aikin SGR, hakan zai taiamka wajen bunkasa manyan gine gine domin karfafa kasuwanci, dunkulewa da ci gaban masana'antu a Afirka."(Maman Ada)