in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: An kaiwa wata coci hari
2017-08-07 09:53:45 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na tarayyar Najeriya suka bayar a jiya Lahadi 6 ga watan nan, wani mutum da ba a san waye ba, ya kai hari wata coci dake jihar Anambra dake kudu maso gabashin kasar, wanda ya haddasa mutuwar mutane 8 tare da raunatar wasu mutane 18.

Wani wanda ya shaida aukuwar lamarin ya bayyana cewa, da misalign karfe 6 na safe ne mutumin ya kutsa cikin cocin, ya harbe wani mutum har lahira, kana ya bude wuta kan sauran mutanen dake cikin coci, harin ya haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama. An ce, mutane fiye da 100 ne ke ibada a cocin a lokacin.

Jami'in hukumar 'yan sanda ta jihar Anambra Garba Umar ya tabbatar da aukuwar harin, amma bai bayyana yawan mutanen da suka mutu ko raunata a sakamakon harin ba. Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike kan harin. An kuma riga an kai mutanen da suka ji raunuka asibitin dake kusa da wurin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China