An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin ma'aikatar yada labarai da al'adu ta Nijeriya da kuma ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin.
Ministan yada labarai da al'adu na Nijeriya Lai Mohammed wanda ya sa hannu a madadin kasarsa, ya ce yarjejeniyar muhimmin ci gaba ne ga huldar diflomasiyyar dake tsakanin Nijeriya da kasar Sin.
Lai Mohammed ya kara da cewa, yarjejeniyar za ta inganta kawance da hulda tsakanin hukumomin watsa labarai na kasashen biyu.
Da farko, mataimakin Daraktan ofishin yada labarai na Majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Weimin, ya ce cimma yarjejeniyar ta bude wani sabon babi na dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannin watsa labarai da al'adu.
Guo Weimin ya ce ma'aikatarsa za ta inganta yada labarai game da Nijeriya a kasar Sin, ya na mai kira ga Ministan na Nijeriya shi ma ya tabbatar da haka a kasarsa. (Fa'iza Mustapha)