in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar gina layin dogo tare da wani kamfanin kasar Sin
2016-11-03 10:16:38 cri
Kasar Zambiya ta cimma a ranar Laraba tare da wani kamfanin gine gine na kasar Sin da wata yarjejeniyar da ta shafi wani sabon shirin gina layin dogo da zai bunkasa harkokin sufuri a wannan kasa dake kudancin Afrika.

Kamfanin gine gine na China Civil Engineering Construction Company (CCECC) zai gina wannan layin dogo na tsawon kilomita 388, bisa jimillar dalar Amurka biliyan 2.3, kuma aikin zai kwashe tsawon shekaru hudu. Haka zalika, layin dogon zai hada birnin Chipata dake gabashin kasar da kuma birnin Serenje dake tsakiya, tare da ratsawa ta birnin Petauke. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China