in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya zanta da takwaransa na Amurka
2016-08-06 13:14:00 cri
Jiya Jumma'a 5 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya zanta da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma yanayin yankin Koriya da dai sauransu.

A yayin zantawar tasu, Wang Yi ya ce, ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi a birnin Hangzhou na kasar Sin za ta kasance wata muhimmiyar dama wajen raya dangantakar kasashen biyu, ya kamata kasashen biyu su dukufa kan wannan batu domin tabbatar da kyawawan sakamakon da za a cimma bisa ganawar shugabannin biyu, da ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba, cikin shekarar da za a gudanar da babban zabe a kasar ta Amurka.

Kaza lika, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Amurka, da ma sauran kasashen da abin ya shafa wajen gudanar da taron kolin kungiyar G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin yadda ya kamata, domin tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arzikin kasa da kasa cikin yanayi mai kyau da kuma mai daidaituwa, kuma, babu shakka, hadin gwiwar mambobin kasashen kungiyar G20 zai taimaka wa gamayyar kasa da kasa a wannan fanni.

A nasa bangare kuma, John Kerry ya ce, ganawar shugabannin Sin da Amurka a birnin Hangzhou za ta dauki muhimmiyar ma'ana ga bangarorin biyu, ya kamata kasashen biyu su dukufa cikin hadin gwiwa, domin cimma nasarar ganawar tasu yadda ya kamata.

Sa'an nan kuma, kasar Amurka tana son hada kai da kasar Sin wajen tabbatar da gudanar da taron kolin kungiyar G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China