Sin da Amurka za su yi hadin gwiwar raya harkokin kiwon lafiya a Saliyo
A jiya Alhamis ne, shehun malami a cibiyar nazarin ayyukan kimiyya ta kasar Sin, kana mataimakin shugaban cibiyar yin rigakafin yaduwar cututtuka ta kasar Sin Gao Fu ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana zabar wurin da za a gina cibiyar nazari da yin rigakafi kan cututtuka da ake samu a yankuna masu zafi a kasar Saliyo, kuma, kasar Sin za ta taimaka wajen gina cibiyar. Sa'an nan, za ta yi hadin gwiwa da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka wajen bunkasa ayyukan kiwon lafiyar al'ummomi a kasar Saliyo. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku