in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron matasan G20 a Shanghai na Sin
2016-07-29 13:37:03 cri

A yau Juma'a da safe ne, aka rufe taron matasan G20 na shekarar 2016 a birnin Shanghai da ke nan kasar Sin, inda aka fitar da wani rahoto bayan tattaunawar da aka yi.

Rahoton ya yi nuni da cewa, muddin ana son cimma burin da aka sanya a gaba a fanni yaki da talauci da samun ci gaba tare, wajibi ne a kara mai da hankali da aikin ba da ilmi, a sa'i daya kuma, ya kamata a taimakawa mabukata kai tsaye, tare kuma da yin amfani da albarkatun da Allah ya horewa al'umma yadda ya kamata.

A fannin tabbatar da adalci da 'yancin zaman takewar al'umma kuwa, rahoton ya bayyana cewa, kamata ya yi a kara ba da muhimmanci kan nuna adalci wajen ba da ilmi yayin da ake kokarin tabbatar da adalci a tsarin zaman takewar al'umma, domin samar da guraben aikin cikin adalci ga kowa.

Wakilan da suka halarci taron sun bayyana cewa, za a kaddamar da taron kolin G20 a kasar Sin, suna fatan matasan za su kara samun damammaki ta hanyar shirya ayyuka iri daban daban kamar irin wannan taron matasan G20, saboda hakan zai bayyana ra'ayoyin matasa kan harkokin da suka fi jawo hankalinsu yadda ya kamata, kana hakan zai samar da damammaki ga matasan ta yadda za su kara ba da gudummuwa kan ci gaban tattalin arzikin duniya da kuma kara kyautata tsarin kasa da kasa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China