Sall yace, Afrika tana maraba da matakan da zasu taimaka wajen habaka cigaban masana'antu a nahiyar, kuma tana fatar taron da za'a gudanar a watan Satumba na kasashen 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya zai waiwayi wannan muhimmin batu.
Shugaban na Senegal ya fada a yayin taron kwamitin shugabanni Afrika karo 27 na taron hadin gwiwar cigaban kasashen Afrika NEPAD karo na 35 a Kigali babban birnin Rwanda cewar, samar da manufofi na hadin gwiwa a tsakanin kasashen nahiyar, zai habaka cigaban masana'antu da inganta rayuwar al'umma mazauna nahiyar.
Yace jagorancin da kasar Sin zata yi ga taron, wata babbar dama ce ta kara hadin gwiwa tsakanin nahiyar Asiya da Afrika wajen bunkasa cigaban ababan more rayuwa.
Ana saran kudurorin da za'a cimma za su bada dama wajen habaka cigaban kimiyya da fasaha, da kirkire kirkire da kananan sana'oi.(Ahmad Fagam)