Fan ya bayyana cewa, Sin ba za ta canza matsayinta kan batun tekun kudancin Sin ba, kuma Sin ba za ta yarda ko amince da sakamakon hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin Sin ba. Jama'ar kasar Sin ba za su mika wuyansu kan kowane irin matsin lamba ba, yayin da rundunar sojan kasar Sin za ta dauki babban nauyi na kiyaye ikon mallakar kasa da tsaron kasa yadda ya kamata.
Fan ya kara da cewa, idan Amurka ta ci gaba da shirinta na girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD a kasar Koriya ta Kudu, hakan zai kawo babbar illa ga tsaron kasar Sin bisa manyan tsare tsare, da tsananta yanayin da ake ciki a zirin Koriya, tare da gurgunta amincewar da ke tsakanin Sin da Amurka bisa manyan tsare tsare.(Fatima)