An rufe taron ministocin kudi da shugabannin babban banki na G20 a zagaye na 3 na shekarar 2016, taron da aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa a birnin Chengdu na nan kasar Sin.
An gabatar da sanarwa game da jigogin taron, inda bangarori daban daban suka kai ga cimma matsaya daya game da daukar karin matakai na kara kwarin gwiwa da ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya gaba.
Taron ya tattauna tare da mai da hankali kan wasu manyan ayyuka, ciki hadda halin da ake ciki a bangaren tattalin arziki, da tsarin da za a bi don samun bunkasuwa mai karfi, mai dorewa da daidaito, da tsarin hada-hadar kudi na duniya, manyan ababen more rayuwa da zuba jari, yi wa hukumomin kudi kwaskwarima, hadin gwiwa tsakanin kasashe daban-daban kan buga haraji, samun bunkasuwar hada-hadar kudi mai dorewa, tattara kudi don yaki da ta'addanci da dai sauransu. Ban da wannan kuma, an ba da tabbaci ga ci gaban da aka samu a wadannan fannoni don share fagen taron koli da za a gudana a birnin Hangzhou.
Ministan baitulmalin kasar Sin Mista Lou Jiwei ya shedawa manema labaru bayan taron cewa, farfadowar tattalin arzikin duniya bai kai hasashen da aka yi a baya ba, inda ake ci gaba da fuskantar kalubale a bangaren halin tattalin arziki da koma bayan tattalin arziki. Saboda ganin haka, ya kamata mambobi kasashen G20 su kara hadin gwiwa da nanata matsaya daya da aka samu a taron G20 da aka yi a birnin Shanghai, haka kuma da ci gaba da daukar matakai da suka dace don karawa juna kwarin gwiwa da kuma ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. (Amina)