in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tattauna harkokin tsaro na wakilan kasashen Afirka, da Sin da kuma Amurka a Togo
2016-07-28 10:48:29 cri
A jiya Laraba ne aka bude kwarya-kwaryar taron tattauna batutuwan da suka jibanci wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afirka, taron da kasashen nahiyar, da kasar Sin da Amurka za su gudanar cikin hadin gwiwa.

Wannan taro na yini biyu, na zuwa ne gabanin taron musamman, wanda kungiyar hadin kan Afirka ta AU za ta gudanar cikin watan Oktoba a birnin Lome. A taron na wannan karo, wakilai mahalartansa za su yi musayar ra'ayi game da batutuwan tsaron kan teku, da inganta harkokin tattalin arziki a gabar tekun Guinea, tare da batun wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel.

Ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey, da hadin gwiwar cibiyar MDD mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel ne suka kira wannan taro, wanda ake sa ran zai bada damar fidda matsaya, game da batutuwan tsaro da suka fi jan hankali a shiyyar.

Yayin bude kwarya-kwaryar taron, Mr. Dussey ya bayyana takaicin sa game da yanayin tabarbarewar tsaro a wasu yankunan nahiyar Afirka.

Taron dai ya hada sassan masu ruwa da tsaki da dama, wadanda suka kunshi wakilan MDD, da na kungiyar AU, da wakilan kasar Sin. Sai kuma wakilan kasar Togo, da na kungiyar ECOWAS da na hukumomin kasar Guinea, da kuma mahukuntan kwamitin lura da tafkunan Chadi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China