Shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su kara amincewar juna. Babban burin Sin shi ne kyautata rayuwar jama'a. Sin ba za ta bi hanyar nuna fifiko a duniya ba, kuma ba za ta keta tsari da dokokin kasa da kasa ba. Babbar moriyar juna tsakanin Sin da Amurka ta fi bambancin ra'ayin dake tsakaninsu, a don haka kamata ya yi kasashen biyu su hada kai, in ji shugaban kasar ta Sin.(Fatima)