Da safiyar yau Laraba ne aka kaddamar da taron matasa na G20 na shekarar 2016, wanda ake yiwa lakabi da Y20 a takaice, taron da aka bude a birnin Shanghai.
Taken taron dai shi ne "kara azama ga matasa wajen kirkiro abubuwa, a kokarin cimma babban buri na bai daya". Wakilan matasa kimani 100 da suka fito daga kasashe mambobin kungiyar G20, da kasashe baki, da kuma hukumomin kasa da kasa. Shekarun matasan dai na tsakanin 18 zuwa 30.
A tsawon taron, wakilan Y20 za su tattauna kan batutuwan da suka shafi kawar da talauci, da samun bunkasuwa tare, da samun adalci a zamantakewar al'umma, da kuma samun daidaito wajen gudanar da hakki. Sa'an nan za a fitar da sanarwar taron, domin gabatar da ita zuwa ga taron share fage kan taron koli na G20 na shekarar 2016. (Kande Gao)