Bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Laos Saleumxay Kommasith, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kare ikon kasashe masu tasowa shi ne nauyin dake bisa wuyanta. Don haka, kasar Sin ta gayyaci kasar Laos, kasa mai rike da shugabancin kungiyar ASEAN da kasar Chadi, kasa mai rike da shugabacin kungiyar AU da kasashen Senegal da Kazakhstan da Masar da kuma sauran manyan kasashe masu tasowa don su halarci taron koli na G20 na Hangzhou. Ban da haka kuma, kasar Thailand, kasa mai rike da shugabancin kungiyar G77 tana fatan za ta iya halartar taron, kasar Sin tana tuntubarta a game da haka. (Lami)