in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya zanta da takwaransa na Amurka
2016-07-07 11:15:31 cri
Jiya Laraba 6 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya zanta da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho, inda suka tattauna kan batun tekun kudancin kasar Sin.

Wang Yi ya ce, a halin yanzu, dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tana bunkasa cikin yanayi mai kyau, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu, a yayin da kuma ake warware sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata, domin ciyar da sabuwar dangantakar manyan kasashe a tsakanin Sin da Amurka gaba.

Haka kuma ya ce, hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin bai dace da tsari da kuma dokokin da abin ya shafa ba, shi ya sa, kotun yanke hukunci ba ta da ikon yin bincike kan wannan batun, kuma dukkan ayyukan da ta yi ba su da wani amfani, sabo da sun saba wa dokoki da kuma harkokin tarihi.

Don gane haka, kasar Sin ba za ta halarci da kuma amincewa da wannan hukuncin da za a yanke ba, domin kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar dokokin teku ta MDD yadda ya kamata, kasar tana kuma sa ran kotun yanke hukunci kan batun za ta iya kawo karshen batun.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce, ana fatan kasar Amurka za ta cika alkawarinta na kaucewa tsoma baki kan batun dake shafar mulkin yankunan kasashen ketare, kar da kawo illa ga cikaken ikon kasar Sin da kuma yanayin tsaron kasar.

A nasa bangare kuma, John Kerrya ya bayyana cewa, kasar Amurka ta gane matsayin kasar Sin kan wannan batu, tana kuma sa ran bangarorin da abin ya shafa za su iya kai zuciya nesa, kasar Amurka da kasar Sin suna da moriya iri daya kan batun kiyaye zaman karko na yankin tekun kudancin kasar Sin, shi ya sa, kasar Amurka tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su iya ci gaba da warware matsalar ta hanyar diflomasiyya da zaman lafiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China