Mr. Adhanom ya bayyana haka ne a yayin babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 69, a cikin tarihin WHO mai shekaru kusan 70, babu wanda ya taba jagorantar kungiyar daga kasashen Afirka, a halin yanzu, Mr. Adhanom ya samu goyon bayan kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU da wasu kasashen Afirka, a watan Janairu na shekarar bana ne kungiyar AU ta zabi Mr. Adhanom a matsayin dan takara daya tilo daga fadin Afirka da zai shiga zaben neman mukamin babban sakataren hukumar WHO.
A wannan rana, Mr. Adhanom ya bayyana a birnin Geneva cewa, idan ya lashe zaben babban sakataren hukumar WHO, zai mai da hankali kan raya ayyukan kiwon lafiya daga tushe a duk fadin duniya, da kuma kyautata kwarewar hukumar WHO wajen fuskantar ayyukan gaggawa, a sa'i daya kuma, zai dukufa wajen kyautata yanayin kiwon lafiyar mata da kananan yara da dai sauransu.
A matsayinsa na shahararren masani kan cutar zazzabin cizon sauro, Mr. Adhanom ya taba zama ministan harkokin kiwon lafiya a kasar ta Habasha daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2012, haka kuma, ya taba zama babban jami'i a Asusun yin rigakafi da ba da agaji kan cutar kanjamau, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro da wasu kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa. (Maryam)