Gidauniyar za ta samar da tallafin kudi mai kwari kuma bisa tsawon lokaci, kana za ta shafi bangarorin daban daban, har da ma kudin karatu na kusan miliyan guda da rabi na kudin Birr a kowa ce shekara zuwa ga dalibai fiye da 100, da kuma wasu dammakin zuwa horo da karatu a kasashen waje.
Duk a wannan rana, kamfanin sadarwa na kasar China ZTE da kamfanin Ethio Teleco sun bada kyautar wani dakin bincike na kimiyyar sadarwa (TIC) ga jami'ar.
Abiy Ahmed, ministan kimiyya da fasaha na kasar Habasha, ya bayyana a albarkacin wannan cewa kamfanonin Sin sun gudanar da ayyuka iri daban daban na cigaban Habasha.
Kafa wannan gidauniya da kyautar dakin binciken TIC na nuna niyyar bangaren kasar Sin na tallafawa kokarin kasar Habasha ga cigaban al'umma, in ji ministan.
La Yifan, jakadan kasar Sin dake Habasha, ya bayyana cewa 'yan kasuwar kasar China dake Habasha, sun taka rawar gani, ta wadannan taimako, da daukar nauyinsu na bil'adama na bayar da wani tallafi a bangaren ilimi, a kokarin halartarsu a cikin ayyuka daban daban na cigaban al'umma.
Dangantaka tsakanin ECCC da AASTU itace irinta ta farko, kuma ECCC ta yi alkawarin fadada hulda tare da sauran makarantun samar da ilimi na kasar. (Maman Ada)