Haka kuma, a wannan ranar kiwon lafiya, hukumar WHO tana mai da hankali kan fuskantar ciwon suga, kana cikin rahoton da ta fidda a ran 6 ga wata, hukumar ta bayyana cewa, cikin kasashe mafi fama da talauci a duniya, kawai kashi daya bisa uku daga cikinsu suna iya ba da jinya ga wadanda suka kamu da ciwon, shi ya sa, hukumar WHO tana yin kira da a karfafa yin rigakafi da kuma ba da jinya kan ciwon suga, ta hanyoyin kyautata yanayin zaman rayuwa da kuma karfafa kwarewar kasa da kasa kan ayyukan da abin ya shafa, ta yadda za a iya sa kaimi ga al'ummomin kasa da kasa da su kara himmatuwa wajen motsa jiki, kyautata tsarin abincinsu, da taimaka wa wadanda suke fama da ciwon wajen samun jinya da kulawa yadda ya kamata. (Maryam)