Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta fitar da wani rahoto a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, daga watan Nuwanba na shekarar da ta wuce zuwa yanzu, yaduwar cutar zazzabin lasser a yammacin Afirka ta haddasa rasuwar mutane kimanin 164 a yankunan, hakan ya sa hukumar ta yi kira da a yi rigakafin dakile yaduwar cutar, ta hanyoyin gudanar da bincike domin hana ci gaba da bazuwar cutar.
Haka zalika, hukumar ta ba da shawara cewa, ya kamata a kebe wuri na musaman da kuma sa ido kan wadanda suka taba kamuwa daga cutar, da ma wadanda suka taba yin mu'amala da majinyatan domin yin bincike na musamman don takawa cutar birki (Maryam)