in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hula 140 na kasar Habasha sun rasu sakamakon harin da masu dauke da makamai na Sudan ta kudu suka kai musu
2016-04-17 19:34:51 cri
Bisa labarin da ma'aikatar yada labaru ta kasar Habasha ta bayar yau Lahadi, an ce, fararen hula 140 na kasar sun mutu sakamakon harin da masu dauke da makamai suka kai a jihar Gambella wadda ke kudu maso yammacin kasar Habasha, kuma ke makwabtaka da kasar Sudan ta kudu.

Hukumar Habasha ta sanar da cewa, wasu dauke da makamai na kasar Sudan ta kudu sun kutsa kai cikin kasar Habasha, sun kuma kai hari kan fararen hula na kasar Habasha. Yanzu sojojin kwantar da kura na kasar Habasha suna farautarsu, kuma ya zuwa yanzu an riga an hallaka masu dauke da makamai 60 na kasar Sudan ta kudu.

Sannan hukumar Habasha ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu babu abin da ya shaida cewa ko wannan lamari yana da alaka da gwamnati ko masu adawa da gwamnati na kasar Sudan ta kudu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China