FAO ta ce, saboda aukuwar yanayi na El Nino mai hana samun amfanin gona, kasar ta sha munanan hasarori ta bangaren sha'anin kiwon dabbobi, haka kuma jama'ar kasar kimanin miliyan 10.2 suna fama da matsalar karancin abinci.
Wakilin FAO dake Habasha ya ce, kasar na fuskantar hali mai tsanani a shekarar 2016, bala'in fari ba ma kawai zai iya hana a yi girbi mai armashi sau biyu a jere ba, hatta ma zai kawo illa ga sha'anin kiwon dabobbi wanda ke dogara ga ciyayi da ruwa. (Amina)