An dauki shekara daya ana kokarin cimma matsaya a kan yarjejeniyar ta hanyar tattuanawa tsakanin bangarorin da abin ya shafa.
Sai a watan Maris din wannan shekarar ne dai kasashen 3 suka rattaba hannu kan amincewa da ka'idojin Khartoum wanda ya ba da damar cigaba da tattaunawa akan siyasa da sauran batutuwan har ma da nazarin batutuwan domin kare kason kasashen 3 a kogin Nile.
Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour a bayanin da yayi ma manema labarai a ranar talatan nan, ya ce cikin yarjejeniyar kasashen 3 sun cimma matsaya kan sanya wani ofishin kasar Faransa ya kammala nazarain da ake yi kan madatsar ruwan na GERD , gami da gaggauta nazarin, da karfafa amincin su da wadannan ka'idojin da kuma aiwatar da taro a kai a kai tsakanin ma'aikatun ruwa da harkokin waje na kasashen 3.
An fitar da jadawalin da za'a kammala nazarin wannan aikin inji Mr Ghandour, a abin da ya bayyana a matsayin abin tarihi wanda ke jaddada kudirin kasashen 3 na shirin gyara tattaunawa da inganta dabarun hadin gwiwwa a dangantakar dake tsakanin su, da kuma ra'ayin da suke da shi tare.
Shi ma a nashi bangaren ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya bayyana jin dadin shi a kan yarjejeniyar, yana mai cewa ta bayyana aniyar kasashen 3 na shawo kan duk wata shinge.(Fatimah Jibril)