Ofishin jakadancin Sin dake kasar Habasha, da ma'aikatar harkokin kudi da hadin gwiwar tattalin arziki ta kasar Habasha, sun gudanar da shawarwarin hadin gwiwar samar da kayayyaki a tsakanin kasashen biyu a karo na farko, yayin zaman da ya gudana a ranar 6 ga watan nan a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Manufar taron dai ta hada da kafa dandalin mu'amala a tsakanin gwamnatoci da kamfanonin kasashen biyu.
Ministan harkokin kudi da hadin gwiwar tattalin arziki na kasar Habasha Ahmed Shide Mohammed, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Habasha na fatan amfani da wannan dama, wajen gano ra'ayoyin kamfanonin kasar Sin, da manufofin da suka shafi hakan, don gudanar da ayyukan hadin gwiwar kasashen biyu yadda ya kamata. (Zainab)