in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: An rasa allurar rigakafin cutar zazzabin Shawara a duniya
2016-04-05 13:56:53 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta fid da wata sanarwa dake cewa, tun daga karshen 2015 da ta gabata ya zuwa wannan lokaci mutane a kalla 198 sun rasa rayukansu a kasar Angola, sakamakon kamuwar da suka yi da cutar zazzabin Shawara.
A kasar Angola inda cutar ta yi barna, an gano wasu mutanen da ke dauke da cutar, kana kuma, wasu masu dauke da cutar sun shiga sauran kasashen Afirka da kasar Sin, duk da cewa a halin yanzu babu allurar rigakafin wannan cuta ta zazzabin Shawara a dukkan duniya.

WHO ta yi nuni da cewa, yin allurar rigakafin cutar zazzabin Shawara ita ce hanya mafi muhimmanci ta dakile cutar, inda kashi 99 cikin dari na mutanen da suka samu allurar ke samun karfin yaki da cutar cikin kwanaki 30.

Ya zuwa karshen watan Maris, WHO da abokan hadin gwiwarta, sun gudanar da allurar rigakafin cutar zazzabin Shawara ga mutane miliyan 5 da dubu 700 a yankin Luanda, wadanda su ne allurar da WHO ta ajiye, bayan da ta fara aiwatar da kudurorin daidaita harkokin kasa da kasa, sai dai ya zuwa yanzu wannan allura ta kare.

Babbar direktar hukumar WHO Margaret Chan, ta fara gudanar da bincike game da halin da ake ciki game da cutar ta zazzabin Shawara a Luanda da kuma gudanar allurar rigakafin cutar a kasar. Kaza lika ta ce Angola, na fuskantar yanayi mafi tsanani game da tinkarar kalubalen da zazzabin Shawara ke haifarwa a cikin shekaru 30 da suka gabata.
(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China