in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan kawo karshen yaduwar ciwon zazzabin sauro a duniya
2016-04-26 11:06:03 cri
A daidai gabar da ake gudanar da bikin ranar rigakafin zazzabin cizon sauro ta duniya, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce akwai kyakkyawan fatan kawar da ciwon zazzabin cizon sauro a duniya baki daya, karkashin shirin da aka tsara a takardar fasahohin ba da jinya da rigakafin ciwon tun daga bana zuwa shekarar 2030 mai zuwa.

Kaza lika, bisa rahoton zazzabin cizon sauron na duniya na bara wanda hukumar WHO ta fitar, an ce an samu babbar raguwa kan adadin masu kamu da ciwon, musamman mutanen da ke rasuwa sakamakon ciwon tun daga shekara ta 2000, sai dai a daya hannun, an cimma wannan nasara ne ta hanyoyin yin amfani da gidan sauro, da bincike, da kuma samar da magungunan cutar ta zazzabin sauro da dai sauran su.

Sai dai ya zuwa yanzu, ana ci gaba da fuskantar babban kalubale kan wannan aiki, sabo da kusan rabin mutanen duniya suna fuskantar kalubalen kamuwa da wannan ciwo, inda a shekarar 2015, aka samu karin mutane miliyan 214 dake kamu da ciwon zazzabin na sauro, yayin da dubu 438 suka rasu sakamakon kamuwa da cutar, kuma galibin su 'yan kasashen dake kudancin Sahara ne.

Kaza lika, a halin yanzu mutane sama da miliyan ba su iya samun kulawa yadda ya kamata, wajen kare kan su daga wannan ciwo. An dai kebe ranar 25 ga watan Afrilun ko wace shekara, a matsayin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya. A bana kuma taken ranar shi ne, "kawo karshen yaduwar zazzabin cizon sauro a duniya". (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China