Zhang Ming ya ce, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Habasha ya kasance abun koyi ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa, kuma abun da ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga raya hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. A watan Disamba na bara, an yi taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika wato FOCAC a birnin johannesburg cikin nasara, kuma abun da ya cusa kuzari wajen raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Habasha, don aiwatar da sakamakon da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin taron, ta yadda za a karfafa hadin gwiwar moriyar juna daga dukkan fannoni a tsakaninsu, tare da kyautata dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, da kawo moriya ga kasashen biyu da jama'arsu.
A nasa bangare kuma, Hailemariam yana mai cewa, kasar Sin abokiya ce kuma babbar kawa ta kasar Habasha, ya kuma jinjina gudummawar da Sin ta bayar wajen raya tattalin arzikin kasar.(Bako)