Mista Liu ya bayyana haka ne a yayin bikin taya murnar ranar ma'adanar kayayyaki ta kasa da kasa da aka yi a cibiyar nazarin kayayyakin tarihi ta jihar Mongolia ta Gida a ran 18 ga wata, kaza lika, ya ce, a kasar Sin a kan yi bukukuwan baje koli har sama da dubu 20 cikin ko wace shekara, inda aka karbi maziyarta kimanin miliyan dari 7.
Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, ya kamata dakunan adanar kayayyakin su kara dukufa wajen raya harkokin al'adu, da kuma dauki alhakin koyarwa matasa ilimi, ta yadda za iya kyautata zaman rayuwar al'ummomin kasar, yayin da ake ciyar da bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma gaba. (Maryam)