Jakadan kasar Sin Xia Huang ya bayyana cewa, za a kafa cibiyar ce domin kiyaye al'adu daban daban daga bacewa.
A jawabinsa Mbagnic Ndiaye ya yi imani cewa, kafuwar cibiyar al'adun kasar Sin za ta kara taimakawa al'ummomin kasar sanin al'adun kasar Sin, tare da ciyar da harkokin al'adun kasar Senegal gaba.
Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kafa cibiyoyin al'adu guda biyar a wasu kasashen Afirka da suka hada da Mauritius, Benin, Tanzania, Nijeriya da kuma Masar. (Maryam)