in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara nuna shirin gaskiya na "Hausawa a Sin" a NTA Hausa
2016-04-13 10:52:31 cri

An fara nuna shirin gaskiya da CRI ya dauka da kuma tsara shi mai taken "Hausawa a Kasar Sin" a NTA Hausa tun ranar 12 zuwa ranar 14 ga watan nan da muke ciki.

Wannan shi ne shirin gaskiya na harshen Hausa na farko da kasar Sin ta tsara da kuma nuna a NTA na Najeriya, kuma shi ne shirin kasar Sin na daban da NTA ta nuna bayan shirye-shiryen wasan kwaikwayo na kasar Sin guda biyu, watau "Soyayyar matasan Beijing" da kuma "Doudou da surukanta".

Sashen Hausa na CRI na kasar Sin ya samar da wannan shiri, wanda ya kunshe sassa guda uku, watau "Dalibta a kasar Sin", "Cinikayya a kasar Sin" da kuma "Garin masoyi ba ya nisa", ko wane kashi na da tsawon mintoci kimanin 20, inda aka bayyana labaran zaman rayuwar Hausawa a nan kasar Sin a fannonin koyon ilmi, da yin ciniki, har ma da aure a tsakanin 'dan Najeriya da wata 'yar kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China