Tawagar ta je Najeriya ne don halartar bikin baje koli karo na 6 na kayayyakin fasaha na nahiyar Afirka da ake shiryawa a Abuja.
A yayin bikin, mai ba da shawara a kan harkokin al'adu na ofishin jakadancin Sin dake tarayyar Najeriya Yan Xiangdong ya bayyana cewa, fasahar hannu wata nau'in fasaha ce ta jama'a, hakan ya sa ya samu amincewa daga jama'a cikin sauki. Masu fasaha daga birnin Nanjing na kasar Sin sun nuna wa al'ummar Najeriya fasahohinsu, ana sa rai wannan matakin zai taimaka wajen cudanyar al'adu a tsakanin kasashen biyu.
Bugu da kari, Mr. Yan ya nuna fatansa na ganin masu fasaha na kasar Sin za su kara komawa kasar ta Najeriya tare da halartar bukukuwan al'adu, ta yadda jama'ar kasar za su samu damar ganin kayayyakin fasaha masu dimbin yawa dake dacewa da rayuwarsu. (Zainab)