Shugaba Xi ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin jawabin da ya gabatar a wani taron mambobin hukumar kula harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS
Ya kuma yi kiran da a kara kokarin yayata al'adun kasar mai tsarin gurguzu, zurfafa yin gyare-gyare a tsarin al'adu, da karfafa tunanin kirkire-kirkiren al'adu na jama'a, matakan da ya yi imanin cewa, za su daga matsayin kasar Sin a bangaren al'adu a idon duniya.
Shugaban ya ce, kamata ya yi a yayata labarun da suka shafi kasar Sin, da manufofinta, ta haka duniya za ta kara fahimtar tsare-tsaren kasar Sin na musamman.
Don haka, ya ce, kamata ya yi a yi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani yadda ya kamata, da kara yin kirkire-kirkire, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabula ta wannan fuska.(Ibrahim)